Posts

Rotation in APC, a gentleman’s agreement – Fashola, party leaders

Image
Private agreement cannot be breached, it must be honoured, says minister • There is an understanding on zoning – Ex-National Vice-Chairman John Alechenu Maiharaji Altine and Chima Azubuike the All Progressives Congress has said it is currently not concerned about the zoning of the presidency in 2023. The Deputy National Publicity Secretary of the APC, Yekini Nabena, who stated this in an interview with The PUNCH on Tuesday, was, however, evasive when asked if the party agreed on zoning before the 2015 elections. Nabena spoke amid disclosure by some chieftains of the APC that before 2015 elections, its leaders had an unwritten agreement on zoning of the presidency. The Minister of Works and Housing, Babatunde Fashola, in an interview with journalists at the ministry headquarters in Abuja on Tuesday, indicated that there was a gentleman agreement on zoning. Others chieftains of the APC including the immediate past National Vice-Chairman (South South), Hilliard Eta, and the Direct

EFCC ta gano makarantar koyar da zamba ta intanet

Image
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya EFCC ta ce ta kama wasu mutum 23 da aka bai wa horo kan zamba ta intanet a jihar Akwa Ibom. Jami'an hukumar sun gano mutanen ne a wani gini da ake zargin masu zamba ta intanet ne suke amfani da shi wajen bai wa mutane horo kan yadda za su kware a harkar damfara. Wajen yana kauyen Ikot Ibiok da ke karamar hukumar Eket ne ajihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajaren ya fitar, ta ce an wadanda ake zargin suna tsakanin shekaru 19 zuwa 35 ne, kuma ana koya musu yadda za su dinga damfara da sata ta intanet. Wannan shi ne waje mafi girma "na makarantar koyar da zamba" da EFF ta gano a kokarinta na hana zamba ta intanet. EFCC ta ce an kama komfuta 34 da wayar hannu 21 a lokacin da aka kai samamen. Za kuma a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike. An bai wa mutane horo kan yadda za su yaudarar mutane ta yadda za s

Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai

Image
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sunan sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya da mambobinta ga majalisar dattijan kasar. Majalisar dattawan kasar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karanta wata wasika da shugaban kasa ya turo mata kan nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya. Sunan wanda shugaban kasar ya mika a matsayin wanda yake so a ba shi shugabancin hukumar Zikrullah Olakunle Hassan wanda ya fito ne daga jihar Osun. Idan har majalisar dattijan ta tabbatar da nadin, to Olakunle ne zai gaji Abdullahi Mukhtar wanda ke kan kujerar tun 2015.Wasu daga cikin wadanda shugaban ya mika sunayensu da za su zama kwamishinoni karkashin hukumar sun hada da Abdullahi Magaji Hardawa wanda ya fito daga Bauchi, sai kuma Nura Hassan Yakasai wanda ya fito daga jihar Kano. Akwai kuma Sheik Momoh Suleman Imonikhe wanda ya fito ne daga jihar Edo. Abdullahi Mukhtar ya jagoranci hukumar alhazai tun watan Mayun shekarar 2015 jhar zuwa yau da aka nada sabo.

Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje kan sabbin masarautu

Image
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi ya roki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje cewa ya janye aniyyarsa ta dawo da sabbin masarautun jihar. Malamin ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da ya aiko wa BBC Hausa.A cikin sakon malamin ya ce: ''Ina rokon Ganduje don Allah, don Annabi ya bar batun (kirkiro sabbin masarautu) kamar yadda kotu ta soke su.'' Ko a kwanakin baya sai da malamin ya nuna rashin jin dadinsa bayan an kafa masarautun a kwanakin baya. Sheikh Dahiru Bauchi ya ce "ina jawo hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa, to ya hakura tun da ( kotu ta mayar) da Kano kamar yadda take shekara dubu da wani abu.''Malamin ya ce "Ganduje ya kammala aikinsa cikin zaman lafiya, ya fi kan ya kammala ana tsine masa.'' Ya kuma ce ''taba fadar Kano, taba mu ne gaba daya 'yan Tijjaniyya ne da masoyanmu.'' Malamin dai ya ce da fatan gwamnan zai ji sha